Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yin Wa’azi ta Wayar Tarho

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yin Wa’azi ta Wayar Tarho

MUHIMMANCINSA: Yin wa’azi ta tarho hanya ce mai muhimmanci na “shaida labari mai daɗi.” (A. M 20:24) * Wannan hanyar tana ba mu damar yin wa’azi ga mutumin da ba za mu iya ganinsa ba.

YADDA ZA MU YI HAKAN:

  • Yin shiri. Ka zaɓi batun da ya dace. Sai ka rubuta abin da kake so ka faɗa. Ban da haka ma, za ka iya shirya gajeren saƙo game da dalilin da ya sa ka yi kira idan maigidan ba ya nan kuma wayar ta bukace ka ka bar saƙo. Zai dace ka zauna a gaban teburi da saƙon da ka rubuta da kuma wasu abubuwan da kake bukata kamar waya da ke da manhajar JW Library® ko kuma ka shiga dandalin jw.org®

  • Ka saki jiki. Ka yi magana yadda ka saba. Ka yi fara’a kuma ka yi kamar mutumin yana ganinka. Kada ka riƙa dakatawa da yawa. Yana da kyau ka yi aikin tare da wani. Idan maigidan ya yi tambaya, ka maimaita tambayar don abokin wa’azinka ya taimaka maka ya nemo amsar

  • Ka yi shiri don ka sake kira. Idan mutumin ya nuna yana son saƙonmu, ka yi masa tambaya kuma ka gaya masa cewa za ka amsa tambayar idan ka sake kiransa. Za ka iya tambayarsa ko zai so ka aika masa saƙon imel ko kuma ka tura masa ɗaya daga cikin littattafanmu da zai karanta. Ƙari ga haka, za ka iya gaya masa cewa za ka tura masa bidiyo ko talifofinmu ta saƙon tes ko e-mail

^ sakin layi na 3 Idan yin wa’azi ta wayar tarho zai yiwu a yankinku, ku yi la’akari da dokar ƙasa a kan yadda za a kāre bayanan mutane.