Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LITTAFIN FIRISTOCI 8-9

Alamar Albarkar Jehobah

Alamar Albarkar Jehobah

8:​6-9, 12; 9:​1-5, 23, 24

Jehobah ya aiko da wuta kuma ya ƙona hadaya da sabbin firistocin suka miƙa masa. Hakan ya nunan cewa Jehobah ya amince da tsarin firistocin. Ƙari ga haka, hakan ya ƙarfafa Isra’ilawa da ke wurin su goyi bayan firistocin. A yau ma, Jehobah yana amfani da Yesu Kristi a matsayin Firist Mafi Girma. (Ibr 9:​11, 12) A 1919, Yesu ya naɗa wani ƙaramin rukunin shafaffun Kiristoci a matsayin ‘bawa mai aminci, mai hikima.’ (Mt 24:45) Me ya tabbatar mana cewa Jehobah yana wa bawan nan albarka, yana tallafa musu kuma ya amince da su?

  • Duk da tsanantawa, bawan nan mai aminci ya ci gaba da tanada mana abubuwan da ke ƙarfafa bangaskiyarmu

  • Kamar yadda aka annabta, ana yin wa’azin labari mai daɗi “ga dukan al’umma.”​—⁠Mt 24:⁠14

Ta yaya za mu goyi bayan bawan nan mai aminci da dukan zuciyarmu?