Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | LITTAFIN FIRISTOCI 4-5

Ku Ba Jehobah Abu Mafi Kyau da Kuke da Shi

Ku Ba Jehobah Abu Mafi Kyau da Kuke da Shi

5:5-7, 11

Talauci bai hana Isra’ilawa neman gafara ba. Waɗanda suka fi talauci a Isra’ila ma za su iya ba da hadaya ga Jehobah, muddin abu mafi kyau da suke da shi ne suka ba shi. Ko da yake za su iya ba da gari, amma Jehobah ya bukace su su ba da gari mai “laushi,” irin wanda suke abinci ma baƙi da shi. (Fa 18:6) A yau ma, Jehobah yana karɓan “hadayar yabo” da muke masa, ko da ayyukan da muke yi a ƙungiyarsa kaɗan ne.​—Ibr 13:15.

Ta yaya hakan zai iya ƙarfafa ka idan ba ka iya yin abubuwan da ka saba yin su, mai yiwuwa saboda rashin lafiya ko kuma ba ka da ƙarfi irin na dā?