Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Ya San Abin da Muke Bukata

Jehobah Ya San Abin da Muke Bukata

Bawan nan mai aminci yana ba mu abinci “a kan lokaci.” Tun da Jehobah ne yake yi wa bawan ja-gora, hakan ya nuna cewa ya san abin da muke bukata. (Mt 24:45) Ban da wasu abubuwa da yake tanada mana, taron yanki da kuma taronmu na tsakiyar mako sun tabbatar mana cewa ya san abin da muke bukata.

KU KALLI BIDIYON NAN RAHOTON KWAMITIN KOYARWA NA 2017, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Wane ne ya kamata mu gode wa saboda taron yanki kuma me ya sa?

  • A wane lokaci ne ake soma shirya taron yanki?

  • Ta yaya ake zaɓan jigon da za a tattauna a taron yanki?

  • Waɗanne irin ayyuka ne ake yi don a shirya taron yanki?

  • Ta yaya ake amfani da tsarin nazarin makarantar Gilead a taronmu na tsakiyar mako?

  • Ta yaya sashe dabam-dabam da ke Bethel suke aiki tare wajen shirya littafin taronmu?

Yaya kake ji game da abubuwan da Jehobah yake mana tanadin su?