’Yan’uwan da suka je taron yanki a Malawi sun taru da yamma suna kallon Tashar JW

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Nuwamba 2019

Yadda Za Mu Yi Wa’azi

Jerin tattaunawa a kan dalilin da ya sa Allah ya halicci duniya da kuma alkawuran da Allah ya yi game da nan gaba.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Kada Ku Kaunaci Duniya Ko Abubuwan da Suke Cikinta

Me zai taimaka mana kada duniya da sha’awoyinta su janye mu daga Jehobah?

RAYUWAR KIRISTA

Ku Guji Shirya Bikin Aure Irin Na Mutanen Duniya

Wadanne ka’idodin Littafin Mai Tsarki ne za su taimaka ma amarya da ango su shirya aurensu yadda zuciyarsu ba za ta dame su ko su yi da-na-sani daga baya ba?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Dole Mu Dāge Sosai Mu Kiyaye Bangaskiyarmu

Ta yaya muke “dāgewa sosai mu kiyaye bangaskiyarmu”?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Na San Ayyukanku”

Yesu ya san duk abin da yake faruwa a ikilisiyoyi kuma shi ne yake wa rukunin dattawa ja-gora.

RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Ya San Abin da Muke Bukata

Me ya sa abubuwan da muke koya a manyan taro su ne abubuwan da muke bukata? Me ya sa muke samun karfafa a taron ikilisiya kuma muke amfana?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Fitowar Mahaya Hudu

A yau muna ganin cikawar annabcin mahaya hudun nan da ke littafin Ru’uyar da Aka Yi Wa Yohanna. Mene ne mahayan suke wakilta?

RAYUWAR KIRISTA

Allah Yana Son Mai Bayarwa da Dadin Rai

Ta yaya za mu ba da gudummawa don a yi amfani da shi a yankinmu da kuma fadin duniya?