Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Albarkun Wa’azi da Amalanke a Fadin Duniya

Albarkun Wa’azi da Amalanke a Fadin Duniya

Littafin Ayyukan Manzanni sura 5 ya nuna cewa Kiristocin ƙarni na farko sukan je haikali inda ake samun jama’a da yawa don su yi musu wa’azi. (A. M 5:​19-21, 42) A yau ma, akwai albarka da yawa da aka samu daga yin wa’azi a inda jama’a suke.

KU KALLI BIDIYON NAN ALBARKUN WA’AZI DA AMALANKE A FAƊIN DUNIYA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • A wace shekara ce aka soma amfani da amalanke a wa’azi kuma ta yaya aka yi hakan?

  • Me ya sa amalanken wa’azi ya fi na teburi amfani sosai?

  • Wane darasi ne muka koya daga labarin ’Yar’uwa Mi Jung You?

  • Mene ne labarin Jacob Salomé ya koya mana game da amfanin yin wa’azi da amalanke?

  • Me labarin Annies da mijinta ya koya mana game da yin wa’azi da kyau sa’ad muke amfani da amalanke?