Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Matasa—Kada Ku Yi Jinkirin Shigan “Kofa Mai-Fadi”

Matasa—Kada Ku Yi Jinkirin Shigan “Kofa Mai-Fadi”

Za mu iya yin tunani cewa ba za mu taɓa shaida “miyagun kwanaki” da tsufa ke kawowa a wannan duniyar Shaiɗan ba. (M. Wa 12:1) Idan kai matashi ne, shin zai dace ka ce za ka faɗaɗa hidimarka a nan gaba tun da yake kana da sauran shekaru da yawa kafin ka tsufa?

“Sa’a da tsautsayi” suna iya shafar kowannenmu, har da matasa. (M. Wa 9:11, Littafi Mai Tsarki) “Ba ku san abin da za ya faru gobe ba.” (Yaƙ 4:14) Saboda haka, kada ku ƙi faɗaɗa hidimarku ba gaira ba dalili. Ku shiga “ƙofa mai-faɗi mai-yalwar aiki” yanzu da yake kuna da zarafin yin haka. (1Ko 16:9) Ba za ku yi da-na-sani ba.

Wasu maƙasudai da za ku iya kafawa:

  • Yin wa’azi a wani yare

  • Hidimar majagaba

  • Halartar makarantun ƙungiyar Jehobah

  • Hidimar gine-gine

  • Hidimar Bethel

  • Hidimar mai kula mai ziyara

Maƙasudaina: