Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 2 KORINTIYAWA 4-6

“Ba Za Mu Fid da Zuciya Ba”

“Ba Za Mu Fid da Zuciya Ba”

4:​16-18

A ce akwai wasu iyalai guda biyu da suke zama a wani gida da ya tsufa sosai. Ɗayan iyalin tana baƙin ciki kullum saboda gidan, ɗayan kuma tana farin ciki domin jim kaɗan za ta ƙaura zuwa wani gida mai kyau.

Ko da yake “har wa yau dukan halitta tana nishi kamar yadda mace mai jin zafin haihuwa takan yi,” bayin Allah suna da bege da yake ƙarfafa su. (Ro 8:22) Mun san cewa wahalolinmu a yau da ma waɗanda mun daɗe muna fama da su ‘ba za su daɗe ba’ domin jim kaɗan, za mu rayu har abada a sabuwar duniya. Idan muka mai da hankali ga albarka da Mulkin Allah zai kawo, za mu yi farin ciki kuma ba za mu fid da rai ba.