Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 2 KORINTIYAWA 7-10

Aikinmu Na Ba da Agaji

Aikinmu Na Ba da Agaji

8:1-4; 9:7

Kiristoci suna da aiki guda biyu da suke yi. Na ɗaya shi ne “hidima ta shirya tsakanin mutane da Allah,” na biyu kuma shi ne “hidimar taimaka wa” ’yan’uwa masu bi. (2Ko 5:​18-20; 8:4) Don haka, taimaka wa ’yan’uwanmu Kiristoci da suke da bukata sashe ne na bautarmu ga Jehobah. Ta yin haka, muna

  • biyan bukatun ’yan’uwan da suke cikin matsala.​—2Ko 9:12a

  • taimaka ma waɗanda suke cikin matsala su soma ayyukansu na ibada kamar nazarin Littafi Mai Tsarki da zuwa taro da kuma fita wa’azi.​—2Ko 9:12b

  • ɗaukaka sunan Jehobah. (2Ko 9:13) Idan mun taimaka wa ’yan’uwanmu da ke da bukata, mutane har ma da maƙiyanmu za su san cewa muna ƙaunar juna