Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

“Abin da Allah Ya Hada . . . ”

“Abin da Allah Ya Hada . . . ”

A bisa Dokar Musa, an bukaci duk wani mutumin da yake so ya kashe aurensa ya rubuta wasiƙar saki ya ba matar. Hakan ya hana mutane kashe aure ba gaira ba dalili. Amma a zamanin Yesu, malaman addinai sun sa kashe aure ya zama abu mai sauƙi. Mutanen suna iya sakan matansu a duk lokacin da suka ga dama. (nwtsty na nazarin Mk 10:​4, 11) Yesu ya taimaka musu su gane cewa Jehobah ne ya shirya aure tsakanin mata da miji. (Mk 10:​2-12) Don haka, mata da miji za su zama “nama ɗaya” kuma su zauna har abada. Abin da zai iya sa a kashe aure shi ne “zina” kamar yadda littafin Matta ya faɗa.​—Mt 19:9.

A yau, mutane suna da ra’ayin Farisawa game da aure ba na Yesu ba. Mutanen duniya suna saurin kashe aure idan suka sami matsala. Amma Kiristoci ma’aurata suna ɗaukan alkawarin da suka yi a lokacin aurensu da muhimmanci kuma suna amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don su magance matsalolinsu. Ku kalli bidiyon nan Idan da Ƙauna da Daraja, Iyalai Za Su Zauna Lafiya, bayan haka, ku amsa tambayoyi na gaba:

  • Ta yaya za ku bi shawarar da ke Misalai 15:1 a aurenku, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?

  • Ta yaya za ku guji matsaloli idan kuka yi amfani da shawarar da ke Misalai 19:11?

  • Idan kuna fuskantar matsaloli a aurenku har kuna tunanin kashe auren, waɗanne tambayoyi ne ya kamata ku yi la’akari da su?

  • Ta yaya ƙa’idar da ke Matta 7:12 za ta taimaka muku ku zama mata da mazan kirki?