Ana wa’azi a kasar Tonga

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Mayu 2018

Yadda Za Mu Yi Wa’azi

Jerin tattaunawa game da nan gaba da kuma duniya.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAHKu Dauki Gungumenku na Azaba, Ku Bi Ni

Ku Dauki Gungumenku na Azaba, Ku Bi Ni

Me ya sa ya kamata Kiristoci su rika addu’a da nazarin Littafi Mai Tsarki da zuwa wa’azi da kuma halartan taro?

RAYUWAR KIRISTA

Ku Koyar da Yaranku Su Rika Bin Kristi

Me ya kamata iyaye su yi don su taimaka wa yaransu su yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma su yi baftisma?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Wahayi da Ke Karfafa Bangaskiya

Ta yaya wannan wahayin ya shafi manzo Bitrus? Mene ne annabcin Littafi Mai Tsarki zai sa mu yi?

RAYUWAR KIRISTA

“Abin da Allah Ya Hada . . . ”

Ya kamata Kiristoci ma’aurata su rika daukan alkawarin da suka yi a lokacin aurensu da muhimmanci sosai. Mata da miji za su iya zauna lafiya idan suna bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Abin da Ta Saka Ya Fi Na Sauran Duka

Wadanne darussa masu kyau ne za mu iya koya daga labari gwauruwa da ta saka anini guda biyu da ba su da daraja?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Kada Ku Ji Tsoron Mutane

Me ya sa manzannin suka tsorata? Bayan an ta da Yesu daga mutuwa, mene ne ya taimaka wa manzannin su daina tsoron mutane kuma su yi wa’azi duk da adawa?

RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Zai Ba Ka Karfin Zuciya

Shin ka taba jin tsoron yin wa’azi ko ka gaya wa mutane cewa kai Mashaidin Jehobah ne a makarantarku? Idan haka ne, ta yaya za ka kasance da karfin hali don ka yi wa’azi?