Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

8-14 ga Mayu

IRMIYA 35-38

8-14 ga Mayu
 •  Waƙa ta 33 da Addu’a

 • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

 • Ebed-melek Misali Ne Na Ƙarfin Hali da Kuma Alheri”: (minti 10)

  • Irm 38:4-6​—Zadakiya ya ji tsoron mutane kuma ya ƙyale maƙiya su jefa Irmiya cikin rijiya mai taɓo don ya mutu (it-2-E 1228 sakin layi na 3)

  • Irm 38:7-10​—Ebed-melek ya yi ƙarfin hali kuma ya nemi hanyar da zai ceci Irmiya (w12 7/1 23 sakin layi na 2-3)

  • Irm 38:11-13​—Ebed-melek ya nuna alheri (w12 7/1 23 sakin layi na 4)

 • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

  • Irm 35:19​—Me ya sa aka albarkaci Rekabawa? (it-2-E 759)

  • Irm 37:21​—Ta yaya Jehobah ya kula da Irmiya, kuma ya hakan zai ƙarfafa mu sa’ad da muke cikin matsala? (w98 2/1 14 sakin layi na 16-17; w95 8/1 5 sakin layi na 6-7)

  • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?

  • Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?

 • Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Irm 36:27–37:2

RAYUWAR KIRISTA

 •  Waƙa ta 127

 • Ku Riƙa Kula da Wuraren Ibadarmu: (minti 15) Sashen tambayoyi ana ba da amsoshi da dattijo zai gudanar. Bayan an nuna bidiyon nan Ku Riƙa Kula da Wuraren Ibadarmu kuma kun amsa tambayoyin, ka ɗan gana da ɗan’uwan da ke wakiltar ikilisiyarku a kwamitin da ke kula da Majami’ar Mulki. (Idan ba ku da wakili a ikilisiyarku, ka gana da mai tsara ayyukan rukunin dattawa. Ka gana da mai kula da gyare-gyare idan ikilisiyarku ce kaɗai take amfani da Majami’ar Mulkin.) Waɗanne gyare-gyare ne aka yi wa Majami’armu kwana-kwanan nan, kuma me aka shirya za a yi nan gaba? Idan wani ya ƙware a fannin gyare-gyare ko kuma yana so ya taimaka, mene ne ya kamata ya yi? Ta yaya dukanmu za mu iya taimaka wajen kula da Majami’ar Mulki?

 • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) kr babi na 12 sakin layi na 9-15, da akwatunan nan “Yadda Aka Kyautata Tsarin Ja-goranci” da “Yadda Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah Take Kula da Al’amuran Mulki

 • Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)

 •  Waƙa ta 125 da Addu’a