Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

29 ga Mayu–4 ga Yuni

IRMIYA 49-50

29 ga Mayu–4 ga Yuni
 •  Waƙa ta 102 da Addu’a

 • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

 • Jehobah Yana Sāka wa Masu Sauƙin Kai Kuma Yana Hukunta Masu Girman Kai”: (minti 10)

  • Irm 50:4-7​—Isra’ilawa masu sauƙin kai za su sami ’yanci kuma su koma Sihiyona

  • Irm 50:29-32​—Za a halaka Babila domin ta yi wa Jehobah raini (it-1-E 54)

  • Irm 50:38, 39​—Ba za a sake zama a Babila ba (jr-E 161 sakin layi na 15; w98 4/1 30 sakin layi na 20)

 • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

  • Irm 49:1, 2​—Me ya sa Jehobah ya tsauta wa Amoriyawa? (it-1-E 94 sakin layi na 6)

  • Irm 49:17, 18​—A wace hanya ce ƙasar Edom ta zama kamar Saduma da Gwamarata, kuma me ya sa? (jr-E 163 sakin layi na 18; ip-2-E 351 sakin layi na 6)

  • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?

  • Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?

 • Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Irm 50:​1-10

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

 • Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) T-32​—Ka yi shiri don koma ziyara.

 • Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) T-32​—Ka tattauna akwatin nan “Ka Yi Tunani a Kan Wannan Tambayar.” Ka yi shiri don ziyara ta gaba.

 • Jawabi: (minti 6 ko ƙasa da hakan) w15 3/15 17-18​—Jigo: Me Ya Sa a Kwanan Nan Ba a Yawan Bayyana a Littattafanmu Cewa Wasu Labaran Littafi Mai Tsarki Suna Wakiltar Muhimman Mutane ko Abubuwa?

RAYUWAR KIRISTA

 •  Waƙa ta 56

 • Ka Cire Gungumen: (minti 15) Ka saka bidiyon nan Ka Cire Gungumen. Bayan haka, ku tattauna tambayoyin nan: Ta yaya wani ɗan’uwa ya kasance da wani hali marar kyau? Me ya taimaka masa ya yi gyara? Ta yaya ya amfana?

 • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) kr babi na 13 sakin layi na 11-23

 • Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)

 •  Waƙa ta 131 da Addu’a