Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 26-33

Ka Roki Jehobah Ya Ba Ka Karfin Zuciya

Ka Roki Jehobah Ya Ba Ka Karfin Zuciya

Dauda ya kasance da ƙarfin zuciya don ya tuna yadda Jehobah cece shi

27:1-3

  • Jehobah ya ceci Dauda daga bakin zaki sa’ad da yake matashi

  • Jehobah ya taimaka wa Dauda ya kashe bear don ya kāre tumakinsa

  • Jehobah ya taimaki Dauda ya ci nasara a kan Goliyat

Me zai taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya kamar Dauda?

27:4, 7, 11

  • Addu’a

  • Wa’azi

  • Halartan taro

  • Nazari na kai da ibada ta iyali

  • Ƙarfafa wasu

  • Tuna yadda Jehobah ya taimaka mana a dā