Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Shin Kana Amfani da JW Library?

Shin Kana Amfani da JW Library?

JW Library wata manhajar kwamfuta ce da ba a sayarwa, kuma za ka iya yin amfani da ita wajen sauko da Littafi Mai Tsarki da littattafai da bidiyoyi da kuma sauti a na’urarka.

YADDA ZA KA SAME TA: Ka shiga intane kuma ka sauko da manhajar JW Library daga wurin da ake kira app store. Ana iya samun manhajar JW Library na na’urori dabam-dabam. Kafin ka fito daga intane, ka buɗe manhajar da ka saukar kuma ka zaɓi abubuwan da kake so ka sauko da su a na’urarka. Da zarar ka sauko da littattafai a na’urarka, za ka iya karanta su ba tare da shigan Intane ba. Da yake ana saka sabbin abubuwa a kai a kai a manhajar JW Library, za ka riƙa shigan intane a kai a kai don ka sauko da su.

ME YA SA KAKE BUKATAR MANHAJAR? Manhajar JW Library za ta ba ka damar yin nazari kai kaɗai da kuma ganin littattafan da ake tattaunawa a taro a sauƙaƙe. Za a iya yin amfani da ita a wa’azi, musamman sa’ad da kuke harkokinku na yau da kullum.