Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 11-18

Wa Za Ya Sauka Cikin Tentin Jehobah?

Wa Za Ya Sauka Cikin Tentin Jehobah?

Kasancewa cikin tentin Jehobah yana nufin zaman abokin Jehobah da dogara da shi da kuma yi masa biyayya. Zabura ta 15 ta nuna abin da Jehobah yake bukata daga abokansa.

WAJIBI NE BAWAN JEHOBAH YA . . .

  • kasance da aminci

  • yi gaskiya, har a cikin zuciyarsa

  • daraja ‘yan’uwansa bayin Jehobah

  • bi umurninsa ko da yin hakan bai da sauƙi

  • taimaka wa masu bukata ba tare da neman wani abu ba

BAWAN JEHOBAH BA YA . . .

  • gulma da tsegumi

  • yi wa mutane mugunta

  • cucin ‘yan’uwansa Kiristoci

  • tarayya da mutanen da ba sa biyayya ko bauta wa Jehobah

  • karɓan cin hanci