Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

HASUMIYAR TSARO

Tambaya: Kana ganin cewa waɗannan kalaman za su cika kuwa?

Nassi: R. Yoh 21:3, 4

Abin da Za Ka Ce: Wannan talifin Hasumiyar Tsaro ta nuna yadda Allah zai cika wannan alkawarin da kuma yadda za ka amfana.

HASUMIYAR TSARO (bangon baya)

Tambaya: Ka yi la’akari da wannan tambayar. [Ka karanta tambaya ta farko da kuma amsoshin da ke shafi na 16.] Mece ce amsarka?

Nassi: Za 83:18

Abin da Za Ka Ce: Wannan talifin ya ba da ƙarin bayani a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da sunan Allah.

MENENE AINIHI LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA?

Tambaya: Wasu mutane suna ganin kamar Allah ne yake mulki da duniya. Amma ka san cewa Littafi Mai Tsarki bai faɗi hakan ba?

Nassi: 1Yo 5:19

Abin da Za Ka Ce: Wannan littafin ya yi bayani dalla-dalla game da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa a kan wannan batun, har da wasu batutuwa.

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.