Wasu ma’aurata suna nazari da na’ura

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Mayu 2016

Gabatarwa

Yadda za a ba da Hasumiyar Tsaro da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Yin Addu’a a Madadin Wasu Yana Faranta wa Jehobah Rai

Allah ya gaya wa Ayuba ya yi addu’a a madadin ‘yan’uwansa marar mutunci guda uku, ko da yake su suka sa ya kara bakin ciki. Ta yaya aka albarkaci Ayuba don bangaskiyarsa da kuma jimirinsa? (Ayuba 38-42)

RAYUWAR KIRISTA

Shin Kana Amfani da JW Library?

Ta yaya za ka saukar da manhajar? Ta yaya za ta taimaka maka a taro da kuma wa’azi?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Daraja Yesu Zai Sa Mu Kasance da Salama da Jehobah

Shin al’ummai sun daraja ikon Yesu ne? Me ya sa yake da muhimmanci mu daraja Sarkin da Allah ya nada? (Zabura 2)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Wa Za Ya Sauka Cikin Tentin Jehobah?

Zabura sura 15 ta kwatanta abin da Jehobah yake bukata daga aminansa.

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Yin Amfani da JW Library

Yadda za mu yi amfani da manhajar don nazari da taro da kuma wa’azi.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Annabcin da Aka Yi Game da Almasihu

Ka ga yadda annabcin da ka yi game da Almasihu a Zabura ta 22 suka cika a kan Yesu.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ka Roki Jehobah Ya Ba Ka Karfin Zuciya

Me zai taimaka mana mu kasance da karfin zuciya kamar Dauda? (Zabura 27)