Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 29-30

Yakub Ya Yi Aure

Yakub Ya Yi Aure

29:18-28

Kafin Yakub ya yi aure, bai san matsalolin da zai fuskanta ba. Rahila da Leya sun zama kishiyoyi. (Fa 29:32; 30:​1, 8) Duk da matsalolin da Yakub ya fuskanta, ya fahimci cewa Jehobah yana tare da shi. (Fa 30:​29, 30, 43) Kuma daga baya, zuriyarsa ce ta zama al’ummar Isra’ila.​—Ru 4:11.

A yau, waɗanda suka yi aure za su fuskanci matsaloli. (1Ko 7:28) Duk da haka, za su iya yin nasara a aurensu kuma su yi zaman lafiya idan suka dogara ga Jehobah kuma suka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.​—K. Ma 3:​5, 6; Afi 5:33.