Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Ka Koya wa Dalibinka Yadda Zai Rika Yin Shiri Don Nazari

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Ka Koya wa Dalibinka Yadda Zai Rika Yin Shiri Don Nazari

MUHIMMANCINSA: Idan daliɓai suka yi shiri kafin nazari, za su fahimci abubuwan da muke koya musu kuma su riƙe a kansu. Idan suka fahimci batun kuma suka riƙe a kansu, hakan zai taimaka musu su sami ci gaba da sauri. Ko bayan sun yi baftisma ma, suna bukatar su riƙa yin shiri don taro da kuma wa’azi idan suna son su ci gaba da ‘yin tsaro.’ (Mt 25:13) Saboda haka, sanin yadda za su riƙa yin nazari da kuma ci gaba da yin hakan zai taimaka musu har ƙarshen rayuwarsu. Don haka, zai dace mu koyar da ɗalibanmu tun da wuri yadda za su riƙa yin shiri don nazarin Littafi Mai Tsarki.

YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:

  • Ka nuna musu yadda za su yi hakan. (Ro 2:21) Ka riƙa shirya nazarin kuma kana la’akari da yanayin ɗalibinka. (km 11/15 3) Ka nuna masa yadda ka saka maki a littafinka

  • Ka ƙarfafa shi ya riƙa yin shiri. Da zarar ka soma nazari da mutumin, zai dace ka gaya masa muhimmancin yin shiri sa’ad da yake nazarin Littafi Mai Tsarki da amfanin yin hakan. Ka shawarce shi a kan yadda zai riƙa samun lokaci don ya yi shirin nazarin. Wasu suna ba wa ɗalibansu littafinsu da suka yi maki sa’ad da suke nazarin don su taimaka wa ɗalibin ya san muhimmancin yin shiri. Ka yaba masa a duk lokacin da ya yi shiri don nazarin

  • Ka nuna masa yadda zai yi shiri don nazarin. Wasu masu shela suna koya wa ɗalibansu yadda za su riƙa yin shiri don nazari da zarar sun soma nazari da su