Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Ta Yaya Za Ka Kaunaci Allah da Kuma Makwabtanka?

Ta Yaya Za Ka Kaunaci Allah da Kuma Makwabtanka?

Ko da yake Kiristoci ba sa bin dokar da aka bayar ta hannun Musa, amma dokar Jehobah da ta ce mu ƙaunace shi da kuma maƙwabtanmu ta bayyana mana abin da yake son bayinsa su yi. (Mt 22:​37-39) Ba a gādar wannan ƙaunar. Maimakon haka, mu ne muke bukatar mu yi ƙoƙari don mu kasance da wannan ƙaunar. Ta yaya za mu yi hakan? Hanya ɗaya ita ce ta karanta Littafi Mai Tsarki. Idan muna yin tunani sosai a kan halayen da Allah yake da su a cikin Littafi Mai Tsarki, za mu ga ‘alherin’ Jehobah. (Za 27:​4, Littafi Mai Tsarki) Hakan zai sa mu ƙara ƙaunar sa kuma mu kasance da hali irin nasa. Ƙari ga haka, zai sa mu bi dokokinsa har da wadda ta ce mu riƙa ƙaunar mutane da gaske. (Yoh 13:​34, 35; 1Yo 5:⁠3) Ga wasu shawarwarin da za su taimaka mana mu ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki:

  • Ka yi tunani sosai. Ka ɗauka cewa kana wajen sa’ad da abin yake faruwa. Me kake gani ko ji? Yaya kake ganin mutanen suke ji a jiki?

  • Ka riƙa canja yadda kake nazarin. Ga wasu misalai: Ka ɗaga muryarka sa’ad da kake karatu ko kuma ka bi karatun sa’ad da kake saurarar karatun sauti. Maimakon ka riƙa karanta sura ɗaya bayan ɗaya, ka karanta game da labarin wani a Littafi Mai Tsarki ko kuma game da wani batu. Alal misali, ka yi amfani da sashe na 4 da 16 na littafin nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah don ka karanta game da Yesu. Ka karanta surar da aka ɗauko nassin yini na ranar gaba ɗaya. Ban da haka, za ka iya karanta littattafan Littafi Mai Tsarki bisa ga lokacin da aka rubuta su.

  • Ka fahimci abin da kake karantawa. Gwanda ka karanta sura ɗaya kuma ka fahimci abin da ka karanta da ka karanta surori da yawa kawai ba tare da fahimta ba. Ka yi la’akari da wannan shawarar. Ka bincika bayanin sosai. Ka yi amfani da taswira da wasu abubuwan bincike. Ka yi bincike a kan bayanin da ba ka fahimta ba. Idan zai yiwu, lokacin da za ka ɗauka kana bimbini ya yi daidai da lokacin da kake yin karatun.