Ana gayyatar mutane zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu a ƙasar Silobiniya

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Maris 2018

Yadda Za Mu Yi Wa’azi

An dauko tattaunawar daga yadda za ba da takardar gayyata zuwa taron tunawa da mutuwar Yesu, da kuma wadannan tambayoyin: Me ya sa Yesu ya mutu? Wane abu ne fansa ta cim ma?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Duk Wanda Yake So Ya Zama Babba A Cikinku, Dole Ne Ya Zama Mai Yi Wa Sauran Hidima”

Shin mun fi mai da hankalin ga wani bangare na ibadarmu da zai sa mutane su rika yabon mu? Kirista mai saukin kai, yakan yi ayyukan da Allah ne kawai ya san da su.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ku Rika Bin Umurnin Dokoki Biyu Mafi Girma

Wadanne dokoki biyu ne Yesu ya ce sun fi girma a Littafi Mai Tsarki? Ta yaya za mu nuna cewa muna bin dokoki biyun nan?

RAYUWAR KIRISTA

Ta Yaya Za Ka Kaunaci Allah da Kuma Makwabtanka?

Wajibi ne mu kaunaci Allah da makwabtanmu. Hanya daya da za mu iya yin hakan ita ce ta wurin karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ka Ci gaba da Yin Kwazo a Wannan Kwanaki na Karshe

Mutane da yawa a yau sun fi mai da hankali a kan kayan duniya kuma hakan ya sa ba sa iya yin wasu abubuwan ibada. Ta yaya halin Kirista da yake kwazo a bautarsa ga Jehobah zai yi dabam da na mutanen duniya?

RAYUWAR KIRISTA

Karshen Wannan Zamani Ya Kusa

Ta yaya kalmomin Yesu suka nuna cewa karshen zamanin nan ya kusa? An tattauna tambayar nan da kuma wasu batu a bidiyon nan Karshen Wannan Zamani Ya Kusa.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Ku Yi Tsaro”

A kwatancin Yesu na budurwai goma, me angon da budurwai masu hikima da marasa hikima suke wakilta? Kuma wane darasi ka koya daga wannan kwatancin?

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Ka Koya wa Dalibinka Yadda Zai Rika Yin Shiri Don Nazari

Tun daga farko, ya kamata mu taimaka wa dalibanmu su ga muhimmancin yin shiri don nazarinsu. Ta yaya za mu yi hakan?