Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Ku Taimaki Iyalinku Su Bauta wa Jehobah

Ku Taimaki Iyalinku Su Bauta wa Jehobah

Jehobah ya aiki Irmiya ya gargaɗi Yahudawa cewa zai halaka su domin sun daina bauta masa. (Irm 13:25) Yaya aka yi mutanen suka nisanta kansu daga bautar Jehobah? Iyalan Isra’ilawa sun yi sanyi a ibadarsu. Babu shakka, magidanta ba su bi umurnin Jehobah da ke littafin Kubawar Shari’a 6:5-7 ba.

A yau, iyalai da suke son Jehobah sosai suna taimaka wa ’yar’uwa a ikilisiya su yi ƙarfi. Magidanta za su iya taimaka wa iyalinsu su bauta wa Jehobah. Ta yaya? Ta wajen yin Ibada ta Iyali a kai a kai da kuma gudanar da ita a hanya mai kyau. (Zab. 22:27) Ku amsa waɗannan tambayoyin bayan kun kalli bidiyon nan Waɗannan Kalmomin . . . Su Zauna a Zuciyarku”—Ganawa da Iyalai:

  • Ta yaya wasu iyalai suka magance ƙalubalen da suka fuskanta sa’ad da suke so su yi ibada ta iyali?

  • Waɗanne amfani ake samu don yin Ibada ta Iyali a kai a kai da kuma gudanar da ita a hanya mai kyau?

  • Waɗanne ƙalubale ne nake fuskanta wajen gudanar da ibada ta iyali kuma yaya nake so in magance su?