Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 12-16

Isra’ilawa Sun Daina Bauta wa Jehobah

Isra’ilawa Sun Daina Bauta wa Jehobah

An ba Irmiya aiki mai wuya da zai nuna cewa Jehobah ya ƙudura niyyar hukunta mutanen Yahuda da Urushalima don taurin kansu.

Irmiya ya sayo ɗamara ta linen

13:1, 2

  • Yadda ya yi ɗamara da ita na wakiltar yadda za su iya ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah

Irmiya ya kai ɗamarar Kogin Yufiretis

13:3-5

  • Ya ɓoye ta cikin wani ƙogon dutse, sai ya dawo Urushalima

Irmiya ya sake koma Kogin Yufiretis don ya ɗauko ɗamarar

13:6, 7

  • Ɗamarar ta lalace

Jehobah ya bayyana batun bayan Irmiya ya kammala aikin

13:8-11

  • Yadda Irmiya ya yi biyayya ga Jehobah duk da cewa aikin yana da wuya, ya taimaka wajen sa Jehobah ya ratsa zukatan mutanen