Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Gabatarwa

Gabatarwa

HASUMIYAR TSARO

Tambaya: A cikin dukan kyaututtuka da Allah ya ba mu, wanne ne ya fi daraja?

Nassi: Yoh 3:16

Abin da Za Ka Ce: Wannan talifin Hasumiyar Tsaro ya nuna dalilin da ya sa Allah ya aiko Yesu duniya don ya mutu a madadinmu da kuma yadda za mu nuna godiya don wannan kyautar.

MENE NE MULKIN ALLAH?

Tambaya: [Ka nuna bangon gaba na warƙar.] Mene ne amsarka ga wannan tambayar? Shin Mulkin Allah wani abu ne da ke cikin zuciyarka? wani wuri ne a sama? ko kuma gwamnati ce a sama?

Nassi: Da 2:44; Ish 9:6

Abin da Za Ka Ce: Wannan warƙar ta nuna albarkar da Mulkin Allah zai kawo maka.

TAKARDAR GAYYATA TA TARON TUNAWA DA MUTUWAR YESU

Abin da Za Ka Ce: Muna gayyatar mutane zuwa wani taro mai muhimmanci da za a yi. [Ka ba maigidan takardar.] Miliyoyin mutane a faɗin duniya za su haɗu a ranar 11 ga Afrilu don su tuna da mutuwar Yesu. Kuma za su ji jawabi daga Littafi Mai Tsarki da zai bayyana yadda za mu amfana daga mutuwarsa. Jawabin kyauta ne. Wannan takardar ta nuna lokaci da kuma wurin da za a yi wannan taron a yankinmu. Muna so ka halarci taron.

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.