Ana gayyatar mutane zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu a Albaniya

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Maris 2017

Gabatarwa

Yadda za a iya ba da mujallar Hasumiyar Tsaro da kuma koyar da gaskiya game da Mulkin Allah. Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Ina Tare da Kai Domin In Cece Ka”

Sa’ad da Jehobah ya zabi Irmiya ya zama annabi, ya ji cewa bai cancanci yin aikin ba. Ta yaya Jehobah ya karfafa shi?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Sun Daina Yin Nufin Allah

Isra’ilawa sun yi tunani cewa hadayar da suke mikawa za ta kāre su duk da miyagun ayyukansu. Irmiya ya fallasa su don zunubinsu da kuma munafuncinsu.

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za a Yi Amfani da Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?

Ku yi amfani da kasidar nan wajen taimaka wa dalibanku su san Shaidun Jehobah kuma ku koya musu game da ayyukanmu da kungiyarmu.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Sai da Taimakon Jehobah Ne Za Mu Yi Nasara

A Isra’ila ta dā, mutanen da suka bi dokar Allah suna samun salama da farin ciki.

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za a Yi Amfani da Ka Saurari Allah

Ka yi amfani da hotuna da kuma nassosi don koyar da gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki ga mutanen da ba su iya karatu ba sosai.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Isra’ilawa Sun Daina Bauta wa Jehobah

Mene ne Jehobah yake nufi sa’ad da ya gaya wa Irmiya ya yi tafiya na mil 300 zuwa Kogin Yufiretis kuma ya boye damara ta linen a wajen?

RAYUWAR KIRISTA

Ku Taimaki Iyalinku Su Bauta wa Jehobah

Idan kuna Ibada ta Iyali mai ma’ana da kuma a kai a kai, hakan zai taimaka wa iyalinku su bauta wa Jehobah. Ta yaya za ka bi da kalubalen da ke tattare da ibada ta iyali?