Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Za Ka Iya Bayyana Imaninka?

Za Ka Iya Bayyana Imaninka?

Idan wani ya tambaye ka dalilin da ya sa ka gaskata cewa Allah ne ya halicci abubuwa, me za ka gaya masa? Idan kana so ka ba da amsa ba tsoro, dole ne ka yi waɗannan abubuwa biyu: Da farko, ya kamata kai da kanka ka san dalilin da ya sa ka gaskata cewa Allah ne ya halicci abubuwa. (Ro 12:​1, 2) Bayan haka, sai ka yi tunani a kan yadda za ka iya bayyana ma wani abin da ka yi imani da shi.​—K. Ma 15:28.

KU KALLI BIDIYON NAN WATA LIKITAR GYARAN KASHI TA BAYYANA IMANINTA DA WANI MASANIN DABBOBI YA BAYYANA IMANINSA DON KU GA DALILAN DA SUKA SA WASU SUKA GASKATA CEWA AKWAI MAHALICCI, SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya sa Irène Hof Laurenceau ta gaskata cewa akwai mahalicci maimakon juyin halitta?

  • Me ya sa Yaroslav Dovhanych ya gaskata cewa akwai mahalicci maimakon juyin halitta?

  • Ta yaya za ka bayyana ma wani dalilin da ya sa ka gaskata cewa akwai mahalicci?

  • Waɗanne abubuwa ne ƙungiyar Jehobah ta tanadar a yarenku da suke taimaka maka ka gaskata cewa akwai mahalicci kuma ka iya bayyana wa mutane dalilin da ya sa ka gaskata cewa Allah ne ya halicci abubuwa?