Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za Mu Yi Amfani da Warkoki a Wa’azi

Yadda Za Mu Yi Amfani da Warkoki a Wa’azi

Tun daga watan Janairu 2018, ana saka bayani a kan yadda za mu yi wa’azi a shafin farko na Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. An ƙarfafa mu mu riƙa tattaunawa da mutane maimakon mu riƙa ba su littattafanmu kawai. Domin a taimaka wa masu shela su iya yin gabatarwa daidai da yanayin mutane, ana wallafa bidiyoyin da suke nuna mana yadda za mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki kaɗai don mu yi wa mutane wa’azi. Shin hakan yana nufin cewa ba za mu riƙa ba mutane littattafanmu ba ne? A’a! Alal misali, warƙoƙi suna taimakawa sosai wajen soma tattaunawa da mutane. Za mu iya yin amfani da bayani na gaba sa’ad da muke amfani da warƙoƙi a wa’azi:

  1. Ka yi wa mutumin tambayoyin da suke bangon gaba na warƙar.

  2. Ka nuna amsar da Littafi Mai Tsarki ya bayar a saman shafi na biyu a warƙar. Idan da lokaci, ka karanta da kuma tattauna abin da ke cikin warƙar.

  3. Ka ba maigidan warƙar kuma ka gaya masa ya karanta.

  4. Kafin ka tafi, ka nuna wa mutumin wurin da ya ce “Ka Yi Tunani A Kan Wannan Tambayar” kuma ka gaya masa za ka dawo don ka ba shi amsar a Littafi Mai Tsarki.

Idan ka dawo, ku tattauna amsar tambayar, sai ka yi wata tambaya da za ku tattauna idan ka sake dawowa. Za ka iya ɗauko tambayar daga dandalinmu ko kuma ka yi tambayar da ke littafin da aka nuna a bangon baya na warƙar. A lokacin da ya dace, sai ka gabatar da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! ko ɗaya daga cikin littattafan da muke nazari da su.