Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYYUKAN MANZANNI 23-24

An Zarge Shi da Ta da Rikici da Kuma Tashin Hankali

An Zarge Shi da Ta da Rikici da Kuma Tashin Hankali

23:12, 16; 24:2, 5, 6, 10-21

Yahudawa da ke Urushalima sun “yi rantsuwa” cewa sai sun kashe Bulus. (A. M 23:12) Amma Jehobah yana son Bulus ya je Roma don ya yi wa’azi. (A. M 23:11) Da yaron ’yar’uwar Bulus ya ji ƙullin da ake yi, sai ya gaya wa Bulus kuma hakan ya sa ba a iya kashe shi ba. (A. M 23:16) Me wannan labarin ya koya maka game da . . .

  • duk wani ƙulli da za a yi don a hana cikar nufin Allah?

  • hanyoyin da Jehobah yake amfani da su don ya taimaka mana?

  • ƙarfin hali?