Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | EZRA 6-10

Jehobah Yana Son Masu Bauta da Zuciya Daya

Jehobah Yana Son Masu Bauta da Zuciya Daya

Ezra ya yi shirye-shirye don ya koma Urushalima

7:6, 22; 8:26, 27

  • Sarki Artaxerxes ya ba Ezra izinin koma Urushalima don ya taimaka a sake soma bautar Jehobah

  • Sarkin ya amince da ‘dukan roƙon’ da Ezra ya yi don gina gidan Jehobah kuma ya ba shi zinariya da azurfa da alkama da inabi da māi da kuma gishiri. Adadinsu sama da dala 100,000,000 ne

Ezra ya dogara ga Jehobah don ya kāre bayinsa

7:13; 8:21-23

  • Koma Urushalima zai yi wuya

  • Sun bi hanya mai haɗari sosai kuma nisanta wataƙila kusan mil 1,000, wato (kilomita 1,600) ce

  • Tafiyar ta kusan wata 4

  • Mutanen da suka dawo suna bukatar bangaskiya da ƙwazo ga bauta ta gaskiya da kuma ƙarfin zuciya

EZRA YA JE DA . . .

Zinariya da azurfa da ya fi talanti 750. Kusan nauyin manya-manyan giwayen Afirka guda 3.

ƘALUBALEN DA MASU DAWOWAN SUKA FUSKANTA . . .

Mahara, hanyar hamada, namomin daji