Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 12-14

Yarjejeniyar da Ta Shafe Ka

Yarjejeniyar da Ta Shafe Ka

12:1-3; 13:14-17

  • Jehobah ya yi wata yarjejeniya ko alkawari da Ibrahim, kuma hakan ya sa zai yiwu Yesu da abokan sarautarsa su yi sarauta daga sama

  • Wannan yarjejeniyar ta soma aiki a shekara 1943 kafin haihuwar Yesu, lokacin da Ibrahim ya ketare Kogin Yufiretis sa’ad da yake zuwa ƙasar Kan’ana

  • Yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki har sai Yesu ya halaka maƙiyan Allah kuma ya kawo albarka ga ’yan Adam a nan duniya

Jehobah ya yi wa Ibrahim albarka don bangaskiyarsa. Idan muka gaskata da alkawuran Jehobah, waɗanne albarka ne za mu samu don yarjejeniyar da Jehobah ya yi da Ibrahim?