Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Kana Amfana Daga Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana?

Kana Amfana Daga Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana?

Shin kana karanta nassi da bayanin da ke Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana don ka kusaci Allah? Idan ba ka yin hakan, shin za ka iya soma yi a kullum? ’Yan’uwa da yawa suna tattauna shi da safe domin su iya tuna darasin da suka koya yayin da suke harkokinsu na yau-da-kullum. (Yos 1:8; Za 119:97) Ta yaya za ka amfana sosai daga Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana? Ka karanta dukan ayoyin da ke nassin yinin don ka san marubucin, da inda ya rubuta nassin, da abin da yake tattaunawa, da dai sauransu. Ka yi tunani a kan labarin Littafi Mai Tsarki da ya koyar da darasin da aka tattauna a ranar. Sai ka yi tunani a kan yadda za ka yi amfani da darasin. Idan kana yanke shawara bisa Kalmar Allah, za ta ja-gorance ka kuma ta sa ka sami albarka.​—Za 119:105.

Iyalin Bethel a duk faɗin duniya sukan yi nazarin littafin nan Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana sa’ad da suke cin abincin safe. A ’yan shekarun nan, ana saka da yawa daga cikin nazarin da iyalin Bethel suke yi a Tashar JW, a sashen bidiyon TSARI NA MUSAMMAN. Za ka iya tuna lokaci na ƙarshe da ka kalli ɗaya daga cikinsu? Mai yiwuwa wasu abubuwan da aka tattauna za su amfane ka sosai. Alal misali, ta yaya labarin Lot zai taimaka maka sa’ad da kake yanke shawara?

KU KALLI BIDIYON NAN KADA KU ƘAUNACI DUNIYA (1YO 2:15), SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce jigon ibada ta safiyar?

  • Ta yaya labarin Lot ya nuna haɗarin son duniya da abin da ke cikinta?​—Fa 13:12; 14:12; 19:​3, 12, 13, 24-26

  • Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah ba duniya ko abubuwan da ke cikinta ba?

Ta yaya zan nuna a harkokina na yau da kullum cewa ina ƙaunar Kalmar Allah?