Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 14-15

Ya Ciyar da Dubbai Ta Hannun Mutane Kalila

Ya Ciyar da Dubbai Ta Hannun Mutane Kalila

Kafin a yi Idin Ƙetarewa a shekara ta 32 bayan haihuwar Yesu, Yesu ya yi wata mu’ujiza wadda an rubuta a littafin Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna.

Ta wannan mu’ujizar, Yesu ya yi wani abu da har yanzu yana yi.

14:​16-21

  • Ko da yake burodi biyar da kifi biyu ne kawai mabiyan Yesu suke da su, Yesu ya umurce su su ciyar da dubban mutane

  • Yesu ya ɗauki burodin da kifin, ya yi addu’a kuma ya rarraba wa mabiyansa. Mabiyansa kuma suka ba wa mutanen

  • Mutanen sun ci sun ƙoshi har abincin ya rage. Yesu ya ciyar da dubban mutane ta wurin mutane kaɗan, wato mabiyansa

  • Yesu ya ce a kwanaki na ƙarshe, zai naɗa wasu da za su riƙa ba da ‘abinci a lotonsa.’​—Mt 24:45

  • A shekara ta 1919, Yesu ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” wato wani ƙaramin rukunin Kiristoci shafaffu da za su ja-goranci “iyalin gidansa,” wato waɗanda za su ci abincin

  • Ta wajen wannan ƙaramin rukunin shafaffu, Yesu yana ciyar da mutane kamar yadda ya yi a ƙarni na farko

Ta yaya zan nuna cewa na sani kuma ina daraja hanyar da Yesu yake amfani da ita wajen taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah?