Ana wa’azi a Kambodiya

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU fabrairu 2018

Yadda Za Mu Yi Wa’azi

An dauko tattaunawar daga tambayar nan: Shawarar Littafi Mai Tsarki tana da amfani a yau kuwa? Ta jitu da kimiyya kuwa? Shawarar Littafi Mai Tsarki tana da amfani a yau kuwa?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Kwatancin Alkama da Zawan

Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya yi kwatancin alkama da zawan? Wane ne mai shuki, da makiyin da kuma masu girbi?

RAYUWAR KIRISTA

Kwatanci Game da Mulki da Kuma Ma’anarsu

Yesu ya yi amfani da kwatanci masu sauki sa’ad da yake koyar da darussa masu muhimmanci. Wadanne darussa ne za mu iya koya daga littafin Matta sura 13?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ya Ciyar da Dubbai Ta Hannun Mutane Kalila

Ko da yake gurasa biyar da kifi biyu ne kawai almajiran Yesu suke da shi, amma Yesu ya ce musu su ciyar da dubban mutane. Me ya faru daga baya? Kuma mene ne hakan yake nufi a gare mu?

RAYUWAR KIRISTA

“Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka”

Yesu ya nuna muhimmancin dokar nan da ta ce “ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.” Shin akwai iyakar inda za mu rika girmama ma iyayenmu ne?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ra’ayin Wa Kake da Shi?

Me za mu yi don mu iya bin ra’ayin Allah? Yesu ya nuna abubuwa uku da za su taimaka mana mu guji tunanin da bai dace ba.

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yin Tambayoyi a Hanyoyin da Suka Dace

Yesu ya yi amfani da tambayoyi don ya koya wa mutane wasu darussa. Ta yaya za mu yi koyi da shi sa’ad da muke wa’azi?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ka Guji Sa Kanka da Kuma Wasu Yin Tuntube

Yesu ya ba da misalai da yawa don ya nuna cewa sa kanmu ko kuma wasu tuntuɓe ba karamin abu ba ne. Mene ne nake yi da zai iya sa ni tuntube?