Wasu ‘yan’uwa mata suna rarraba ƙasidar nan Ka Saurari Allah a Indonisiya

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU fabrairu 2016

Gabatarwa

Hanyoyin gabatar da Awake! da kuma kasidar nan Ka Saurari Allah! Ka yi amfani da misalan gabatarwar da aka ba da don ka rubuta naka.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Nehemiya Ya So Bauta ta Gaskiya

Ka yi tunani a kan yadda Nehemiya ya kuduri niyyar sa a sake soma bauta ta gaskiya. (Nehemiya 1-4)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Nehemiya Mai Kula Ne da Ya Kware

Nehemiya ya taimaka wa Isra’ilawa su yi farin cikin yin bauta ta gaskiya. Ka yi tunani a kan abubuwan da suka faru a Urushalima a watan Tishri na shekara ta 455 K.H.Y. (Nehemiya 8:1-18)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Amintattun Bayin Jehobah Suna Tallafa wa Tsarin Allah

A zamanin Nehemiya, mutanen Jehobah sun tallafa wa bauta ta gaskiya da yardan rai. (Nehemiya 9-11)

RAYUWAR KIRISTA

Rayuwa Mafi Inganci

Matasa da suke bauta wa Jehobah suna da hanyoyi da dama na yin rayuwa mafi inganci. Ka yi amfani da tambayoyin nan wajen tattauna bidiyon nan.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Darussan da Za Mu Koya Daga Nehemiya

Ka ga irin kwazon da Nehemiya ya yi don kare bauta ta gaskiya. (Nehemiya 12-13)

RAYUWAR KIRISTA

Ku Gayyaci Kowa a Yankinku Zuwa Taron Tuna da Mutuwar Yesu!

Yadda za a rarraba takardar gayyatar Taron Tuna da Mutuwar Yesu na 2016. Ka bi shawarar da ke nan don ka taimaki mutanen da ke son sakonmu.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Esther Ta Kare Mutanen Allah

Ka yi tunani a kan yadda ta yi gaba gadi don ta kare bayin Jehobah. (Esther 1-5)