Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZAFANIYA 1–HAGGAI 2

Ku Bidi Jehobah Kafin Ranar Fushinsa

Ku Bidi Jehobah Kafin Ranar Fushinsa

Zep 2:2, 3

Ba yin alkawari cewa za mu bauta wa Jehobah kaɗai muke bukata mu yi ba idan muna so mu tsira a ranar fushinsa. Wajibi ne mu bi umurnin da Zafaniya ya ba Isra’ilawa.

  • Ku biɗi Ubangiji: Ku kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah a matsayin mutanen da ke ƙungiyarsa

  • Ku biɗi adalci: Ku riƙa bin ƙa’idodin Jehobah sosai

  • Ku biɗi tawali’u: Ku yi nufin Allah cikin sauƙin kai kuma ku amince idan ya yi muku gyara

Ta yaya zan biɗi Jehobah da adalci da kuma tawali’u sosai?