Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Mece ce Kauna ta Gaskiya?

Mece ce Kauna ta Gaskiya?

Jehobah ya shirya aure ne don mata da miji su kasance tare har abada. (Fa 2:​22-24) Zina ce kaɗai za ta iya sa ma’aurata su kashe aurensu. (Mal 2:16; Mt 19:9) Tun da Jehobah yana so ma’aurata su riƙa jin daɗin aurensu, shi ya sa ya yi tanadin ƙa’idodin da za su taimaka wa Kiristoci su zaɓi aboki ko abokiyar aure nagari kuma su ji daɗin aurensu.​—M. Wa 5:​4-6.

KU KALLI BIDIYON NAN MECE CE ƘAUNA TA GASKIYA?, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Ta yaya shawarar da Frank da Bonnie suka ba ʼyarsu ta nuna cewa suna da hikima kuma suna ƙaunarta?

  • Me ya sa bai dace mu yi tunanin cewa za mu iya canja halin mutumin da muke so mu aura ba?

  • Wace shawara mai kyau ce Paul da Priscilla suka ba Liz?

  • Me ya sa Zach da Megan suka sami matsala a aurensu?

  • Waɗanne maƙasudai ne John da Liz suke da shi?

  • Me ya sa ya kamata ka san “ɓoyayyen mutum na zuciya,” wato halin mutum kafin ka yi wa’adin aure? (1Bi 3:4)

  • Mece ce ƙauna ta gaskiya? (1Ko 13:​4-8)