Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 11-16

Sanin Jehobah Zai Cika Duniya

Sanin Jehobah Zai Cika Duniya

11:6-9

Yadda wannan annabcin ya cika a kan Isra’ilawa

  • Isra’ilawa ba su ji tsoron namomin daji ko mugayen mutane sa’ad da suke dawowa daga bauta a Babila ko kuma sa’ad da suke ƙasarsu ba.—Ezr 8:21, 22

Yadda wannan annabcin yake cika a zamaninmu

  • Sanin Jehobah ya canja halayen mutane. Mutanen da ke son faɗa sosai a dā sun zama masu son kwanciyar hankali. Sanin Allah ya kuma sa mu kasance cikin yanayin salama a ƙungiyar Jehobah

Yadda wannan annabcin zai cika a nan gaba

  • Duniya gabaki ɗaya za ta zama aljanna kuma salama za ka kasance a ko’ina yadda Allah ya so tun asali. ‘Yan Adam da kuma dabbobi ba za su tayar da hankula ba

Sanin Allah ya sa Bulus ya canja salon rayuwarsa

  • Kafin Saul ya zama Bulus, yana da mugayen halaye kamar dabba.—1Ti 1:13

  • Amma sanin Allah ya sa ya canja halayensa.—Kol 3:8-10