Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 6-10

Almasihu Ya Cika Annabci

Almasihu Ya Cika Annabci
DUBA

Shekaru da yawa kafin a haifi Yesu, Ishaya ya annabta cewa Almasihu zai yi wa’azi a “ƙetaren Urdun, Galilee na al’ummai.” Yesu ya cika wannan annabcin sa’ad da ya je dukan yankuna na Galili yana wa’azin bishara kuma yana koyarwa.—Ish 9:1, 2.

  • Ya yi mu’ujizarsa ta farko—Yoh 2:1-11 (Kana)

  • Ya zaɓi manzanninsa—Mk 3:13, 14 (kusa da Kafarnahum)

  • Ya yi Huɗuba a kan dutse—Mt 5:1–7:27 (kusa da Kafarnahum)

  • Ya ta da yaron wata gwauruwa daga mutuwa—Lu 7:11-17 (Nayin)

  • Bayan ya tashi daga mutuwa, ya bayyana ga mabiyansa guda 500—1Ko 15:6 (Galili)