Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 17-18

Ku Koyar da Wasu Kuma Ku Ba Su Aiki

Ku Koyar da Wasu Kuma Ku Ba Su Aiki

18:17, 18, 21, 22, 24, 25

Idan ’yan’uwa maza suka koyar da matasa kuma suka ba su aiki, hakan zai nuna cewa suna da sanin ya kamata, suna da ƙauna kuma suna hangen nesa. Ta yaya za su yi hakan?

  • Ku zaɓi waɗanda suka cancanci a ba su ƙarin aiki

  • Ku bayyana musu dalla-dalla yadda za su yi aikin

  • Ku tanada musu abin da suke bukata don su yi aikin

  • Ku riƙa lura da yadda ɗalibin yake yin aikin kuma ku gaya masa cewa zai iya yin aikin

KA TAMBAYI KANKA, ‘Wane aiki ne zan so in ba ma wasu?’