Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Ku Yabi Jehobah ta Yin Hidimar Majagaba

Ku Yabi Jehobah ta Yin Hidimar Majagaba

Isra’ilawa suna da dalilai masu kyau na yabon Jehobah. Ya fitar da su daga Masar kuma ya cece su daga hannun Fir’auna da sojojinsa. (Fit 15:​1, 2) Har yanzu Jehobah bai daina yi wa bayinsa alheri ba. Ta yaya za mu gode masa?​—Za 116:12.

Hanya ɗaya da za mu yi hakan ita ce ta yin hidimar majagaba na ɗan lokaci ko na kullum. Ku roƙi Allah ya ba ku niyya da kuma ƙarfin yin wannan hidimar. (Fib 2:13) ’Yan’uwa da yawa sukan soma da yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Idan kana hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Maris da Afrilu ko kuma lokacin ziyarar mai kula da da’irarku, za ka iya ba da awa 30 zuwa 50. Bayan ka ji daɗin yin hidimar majagaba na ɗan lokaci, mai yiwuwa hakan zai sa ka so yin hidimar majagaba na kullum. Har waɗanda suke da yawan aiki ma da marasa lafiya sun iya yin hidimar majagaba na kullum. (mwb16.07 8) Babu shakka, Jehobah ya cancanci duk ƙoƙarin da muke yi don mu yabe shi!​—1Tar 16:25.

KU KALLI BIDIYON NAN ’YAN’UWA MATA UKU A MONGOLIA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Waɗanne matsaloli ne ’yan’uwa ukun nan suka magance don su iya yin hidimar majagaba?

  • Waɗanne albarku ne suka samu?

  • Wane ƙarin gata ne suka samu don sun yi hidimar majagaba?

  • Ta yaya wasu suka amfana daga misalinsu?