Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Matasa​—Ku Zama “da Kwazon Yin Ayyukan Kirki”

Matasa​—Ku Zama “da Kwazon Yin Ayyukan Kirki”

A cikin huraren wasiƙa da Bulus ya aika ma Titus, Bulus ya ƙarfafa matasa har da Titus cewa a duk abin da suke yi, su nuna cewa su masu yin “aiki nagari” ne. (Tit 2:​6, 7) Daga baya ya sake faɗa a surar cewa an tsarkake bayin Jehobah domin su yi “ƙwazon yin ayyukan kirki.” (Tit 2:14) Ɗaya daga cikin ayyukan kirki da matasa za su iya yi shi ne, wa’azi da kuma koyarwa game da Mulkin Allah. Idan kai matashi ne, za ka iya yin amfani da ƙarfinka don ka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci ko na kullum.​—K. Ma 20:29.

Idan kana son ka yi hidimar majagaba, ka shirya ayyukanka don ka iya yin hakan. (Lu 14:​28-30) Alal misali, za ka iya shirya yadda za ka riƙa samun kuɗin biyan bukata da kuma yadda za ka riƙa cika sa’o’in da ake bukata. Ka yi addu’a ga Jehobah a kan shawarar da kake son ka yanke. (Za 37:5) Ka kuma gaya ma iyayenka da kuma ’yan’uwa da suka yi nasara a hidimar game da shawarar da kake son ka yanke. Sa’an nan ka ɗauki matakan da za su sa ka iya cim ma makasudinka. Jehobah zai albarkace ka don ƙoƙarin da ka yi!

KU KALLI BIDIYON NAN WASU MATASAN DA SUKA ƊAUKAKA JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne matsaloli ne wasu ’yan’uwa suka jimre don su iya yin hidimar majagaba?

  • Ta yaya iyaye za su iya taimaka ma yaransu su iya yin hidimar majagaba?

  • Me ya sa yake da kyau mu tsara lokutan da za mu riƙa fita wa’azi?

  • Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su taimaka da kuma ƙarfafa majagaba?

  • Wace albarka ce majagaba suke samuwa?

Mene ne zan yi don in cim ma makasudina na yin hidimar majagaba?