Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Yaushe Ne Zan Sake Yin Hidimar Majagaba Na Dan Lokaci?

Yaushe Ne Zan Sake Yin Hidimar Majagaba Na Dan Lokaci?

Wahayin da Ezekiyel ya gani game da haikali ya nuna cewa mutanen Jehobah za su ba da hadaya da yardar ransu. Amma, ta yaya ne za mu iya ba da hadaya ta yabo ga Jehobah?​—Ibran. 13:15, 16.

Hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Daga watan Satumba na 2017 zuwa Agusta na 2018, akwai watanni da dama da suke da Lahadi biyar da Asabar biyar. Hakan zai taimaka wa ’yan’uwan da ranakun Asabar da Lahadi ne suke fita wa’azi. Ƙari ga haka, masu shela za su iya yin wa’azi na sa’o’i 30 ko 50 a watan Maris da Afrilu ko kuma a lokacin da mai kula da da’ira ya ziyarce su.

Me za mu yi idan yanayinmu ya hana mu yin hidimar majagaba na ɗan lokaci? Za mu iya inganta yadda muke yin wa’azi da kuma ƙara sa’o’in da muke yin wa’azi. Kome yanayinmu, bari ƙaunarmu ga Jehobah ta motsa mu mu yi iya ƙoƙarinmu a watan Satumba na 2017 zuwa Agusta na 2018!​—Hos. 14:2.

Ta yaya zan yi ƙwazo a wa’azi kamar Sabina Hernández?

KU KALLI BIDIYON NAN DA TAIMAKON JEHOBAH, ZAN IYA YIN KOME, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Mene ne ya sa Sabina ta faɗaɗa hidimarta ga Jehobah?

  • Ta yaya abin da Sabina ta yi ya ƙarfafa ka?

  • A wane wata ne za ka so ka yi hidimar majagaba na ɗan lokaci?