Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Wa’azi da Koyarwa Suna da Muhimmanci Wajen Mai da Mutane Almajiran Yesu

Wa’azi da Koyarwa Suna da Muhimmanci Wajen Mai da Mutane Almajiran Yesu

Yesu ya umurci mabiyansa su je su almajirantar da mutane. (Mt 28:19) Yin hakan ya ƙunshi wa’azi da kuma koyarwa. Don haka, ya kamata mu yi wa kanmu wannan tambayar a wasu lokuta, ‘Ta yaya zan inganta yadda nake koyar da mutane?’

WA’AZI

Maimakon mu jira mutane su zo su same mu, zai dace mu yi iya ƙoƙarinmu don mu nemi mutanen da suka “cancanta.” (Mt 10:11) Idan muka fita wa’azi, shin muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi wa’azi ga dukan ‘mutane da muka gani’? (A. M. 17:17) Manzo Bulus ya yi wa’azi da ƙwazo kuma hakan ne ya sa Lidiya ta zama almajirar Yesu.​—A. M. 16:​13-15.

“Ka shuka iri da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka” (M. Wa 11:​6, Littafi Mai Tsarki)

KU KALLI BIDIYON NAN, KU CI-GABA DA YIN WA’AZI BABU ‘FASHI’​—SA’AD DA KUKA SAMI DAMA A DUK INDA KUKE DA WA’AZI NA GIDA-GIDA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Ta yaya Samuel ya yi ƙoƙarin shuka iri na gaskiya a inda yake aiki?

  • Me ya sa ya kamata mu riƙa yin wa’azi ta hanyoyi dabam-dabam?

  • Su wa za ka yi musu wa’azi a inda kake ayyukanka na yau da kullum?

KOYARWA

Taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu ya wuce ba su littattafanmu kawai. Dole mu sake komawa mu yi nazari da su idan muna son su yi amfani da abubuwan da suke koya. (1Ko 3:​6-9) To me zai faru idan mun yi iya ƙoƙarinmu amma duk da haka, mutumin ba ya samun ci gaba sosai? (Mt 13:​19-22) Sai mu ci gaba da neman mutane masu zuciya kamar “ƙasa mai-kyau” a kwatancin da Yesu ya yi.​—⁠Mt 13:23; A. M. 13:⁠48.

“Ni na dasa, Afollos ya yi ban ruwa; amma Allah ne ya ba da amfani” (1Ko 3:6)

KU KALLI BIDIYON NAN KU CI-GABA DA YIN WA’AZI BABU ‘FASHI’​—YIN WA’AZI GA JAMA’A DA YIN NAZARI DA MUTANE, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Ta yaya Solomon da Mary suka taimaka wa Ezekiel da Abigail su soma bauta ma Allah?

  • Mene ne ya kamata ya zama ainihin burinmu yayin da muke yin wa’azi?

  • Ta yaya za mu mai da hankali ga koya wa mutane Kalmar Allah?