Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Ku Yi Amfani da Littattafai da Bidiyoyinmu na Wa’azi da Kyau

Ku Yi Amfani da Littattafai da Bidiyoyinmu na Wa’azi da Kyau

Yin almajiranci yana kama da gina gida. Don mu iya yin ginin da kyau, dole ne mu koyi yadda za mu yi amfani da littattafai da bidiyoyinmu na wa’azi da kyau, musamman ma Littafi Mai Tsarki. (2Ti 2:15) Ƙari ga haka, ya kamata mu riƙa amfani da littattafai da bidiyoyin da muke wa’azi da su da kyau don mu iya taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu. *

Ta yaya za ka kyautata yadda kake amfani da littattafai da bidiyoyinmu na wa’azi? (1) Ka tambayi dattijon da yake kula da rukunin wa’azinku, (2) ka fita wa’azi tare da wani mai shela da ya ƙware ko kuma wani majagaba, (3) ka ci gaba da kwaikwayon yadda za ka yi wa’azi. Idan ka koya kuma ka ƙware a yin wa’azi, za ka riƙa jin daɗin yi wa mutane wa’azi.

MUJALLU

ƘASIDU

LITTATTAFAI

WARKOKI

BIDIYOYI

TAKARDAR GAYYATA

KATIN JW

^ sakin layi na 3 Sauran littattafan da ba sa cikin littattafai da muke wa’azi da su, an rubuta su ne don wasu mutane na musamman. Muna iya amfani da su ga mutanen da aka rubuta domin su.