Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Sabon Talifi don Soma Tattaunawa da Mutane

Sabon Talifi don Soma Tattaunawa da Mutane

Tun daga watan Maris na 2016, an soma wallafa wani talifi a bangon baya na Hasumiyar Tsaro ta wa’azi na Hausa mai jigo, “Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?” An shirya wannan talifin ne don ya taimaka mana mu san yadda za mu soma tattauna wasu batutuwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki da mutane. Yana da irin fasalin warƙoƙinmu. An saka tambayoyin da za a yi wa mutane da amsar da Littafi Mai Tsarki ya bayar da kuma wasu ƙarin bayanai.

Sau da yawa, tattaunawa mai daɗi daga Littafi Mai Tsarki yana sa mutane su amince a yi nazari da su. Saboda haka, ku yi amfani da wannan sabon talifin wajen taimaka wa mutane da yawa su ƙulla abota da Allah.—Mt 5:6.

YADDA ZA A YI AMFANI DA WANNAN TALIFIN:

  1. Ka tambayi mutumin ra’ayinsa a kan ɗaya daga cikin tambayoyin

  2. Ka saurari amsar da ya bayar kuma ka gode masa

  3. Ka karanta nassin da ke ƙarƙashin ƙaramin jigon nan “Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce,” kuma ka tambayi ra’ayinsa game da ayar. Idan yana da lokaci, ku tattaunawa batun da ke ƙaramin jigon nan “Me Kuma Za Mu Iya Koya Daga Littafi Mai Tsarki?”

  4. Ka ba da mujallar

  5. Ka shirya yadda za ka sake dawowa don ku tattauna tambaya ta biyu