A2
Abubuwan da Suke Cikin Wannan Fassarar
An fitar da juyin Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya (Matiyu-Ruꞌuya ta Yohanna) na Turanci a shekara ta 1950, kuma an wallafa cikakken juyin Littafi Mai Tsarki—Fassarar Sabuwar Duniya na Turanci a shekara ta 1961. Tun daga lokacin, miliyoyin masu karatu cikin yaruka fiye da ɗari biyu da goma sun amfana daga Nassosi Masu Tsarki da aka fassara da kyau daga yaruka na asali kuma suna da sauƙin karantawa.
Kwamitin Juyin Fassarar Sabuwar Duniya ya fahimci cewa ana bukatar fassarar da za ta ratsa zukatan masu karatu a yau. Don ya cim ma wannan maƙasudin, kwamitin ya yi abubuwan nan da ke gaba:
-
Amfani da kalmomi da furuci na zamani da za a iya fahimta. Alal misali, furucin nan “dogon jimrewa” zai iya ba da maꞌana da ba daidai ba cewa “mutum ya daɗe yana shan wahala.” Amma ainihin abin da ake nufin shi ne mutum ya kame kansa, kuma kalmar da za ta bayyana wannan maꞌanar da kyau ita ce “haƙuri.” (Galatiyawa 5:22) A wannan juyin, an mai da kalmar nan “fasikanci” zuwa “lalata;” “nishatsai” kuma mun mai da ita “bukukuwan iskanci.”—Galatiyawa 5:19-21.
A Ibrananci da yaren Girka na dā, kalmar nan “iri” tana iya nufin irin da ake shukawa ko zuriyar ꞌyanꞌadam ko kuma maniyyi. Amma da yake a Hausa ba a yawan amfani da kalmar nan “iri” saꞌad da ake magana game da ꞌyanꞌadam, an canja kalmar zuwa wasu kalmomi da suka ba da maꞌanar abin da ake magana a kai.—Farawa 1:11; 22:17; 48:4; Matiyu 22:24; Yohanna 8:37.
-
Furucin Littafi Mai Tsarki da aka ba da ƙarin haske a kai. A yawancin lokuta, wasu furuci da aka yi amfani da su a cikin wasu juyin Littafi Mai Tsarki suna bukatar ƙarin haske domin a fahimce su da kyau. Alal misali, a cikin Littafi Mai Tsarki, an yi amfani da kalmar Ibranancin nan “Sheol” da kuma na yaren Girka “Hades” saꞌad da ake maganar kabari. Mutane da yawa ba su san waɗannan kalmomin ba, kuma “Hades” tana da maꞌana biyu saboda abin da mutanen Girka suka yi imani da shi. Saboda haka, an canja kalmomin nan da kalmomin da suka yi daidai da ainihin abin marubutan Littafi Mai Tsarki suke nufi, wato “Kabari.” An saka “Sheol” da “Hades” a cikin ƙarin bayani.—Zabura 16:10; Ayyukan Manzanni 2:27.
Juyin Littafi Mai Tsarki da yawa a Hausa sun ce an kashe Yesu a kan “gicciye.” Kalmar nan a yaren Girka, wato stau·rosʹ tana nufin gungume ko kuma katako. An kashe Yesu a kan gungume da ke tsaye. Saboda haka, a wannan juyin an yi amfani da kalmar nan “gungume” don a bayyana abin da kalmar a yaren Girka take nufi.—Matiyu 27:31.
Ƙari ga haka, wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun fassara kalmar nan Gehenna zuwa “Gidan Wuta,” kuma hakan zai sa mutane su ga kamar wani wuri ne da ake azabtar da mutane a cikin wuta. Amma a wannan juyin, an yi amfani da asalin kalmar, kuma an sa ƙarin bayani da ke gaya wa masu karatu su duba maꞌanar Gehenna a sashen Maꞌanar Kalmomi.—Matiyu 5:22; Markus 9:43; Luka 12:5.
-
Sauƙin karantawa. An yi ƙoƙari sosai don a yi amfani da kalmomi da furuci waɗanda suke da sauƙin ganewa kuma za su sa mutane su so karatu ba tare da an canja maꞌanar da ke yare na asali ba. A dā, akwai wasu furuci da aka fassara su daidai yadda suke daga yare na asali waɗanda suke da wuyan fahimta, amma yanzu an canja su. Alal misali, wani juyin Littafi Mai Tsarki a Hausa ya fassara 1 Korintiyawa 7:36-38 ta wurin yin amfani da furuci da kalmomi da aka yi amfani da su a yare na asali. A aya ta 36, juyin ya ce: “Amma idan kowane mutum yana tsammani yana yin abin da ba ya dace ga ɗiyatasa wadda ta ke budurwa ba.” Amma ga yadda aka fassara shi a wannan juyin don a nuna ainihin abin da ake nufi don ya yi sauƙin fahimta da kuma sauƙin karantawa: “Idan wani yana ganin yana yin abin da bai dace ba saboda bai yi aure ba.”
An yi adduꞌa sosai kuma an mai da hankali yayin da ake fassara dukan ayoyin da ke cikin wannan juyin Littafi Mai Tsarki, an kuma daraja aiki mai kyau da Kwamitin Juyin Fassarar Sabuwar Duniya ya yi.
Wasu abubuwa da ke cikin wannan juyin:
Wannan juyin Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙarin bayanai dabam-dabam. Ga ire-iren ƙarin bayanai da aka yi amfani da su:
-
“Ko kuma” Wata hanya dabam da za a iya fassara furucin daga yaren Girka kuma ba zai canja maꞌanar ba.—Matiyu 5:3, ƙarin bayani da ke kan “ja-gorancin Allah.”
-
“Yana kuma iya nufin” Wata hanya dabam da mai yiwuwa za a iya fahimtar abin da aka fassara.—Luka 12:11, ƙarin bayani da ke kan “taron jamaꞌa.”
-
“A yaren Girka” Fassarar da aka yi kalma bayan kalma ko a zahiri ko kuma maꞌanar wani furuci daga yaren Girka.—Ayyukan Manzanni 1:21, ƙarin bayani da ke kan “yake yin ayyukansa.”
-
Maꞌana da wasu muhimman bayanai Wannan ƙarin bayanin yana ba da maꞌanar suna; ko bayanai a kan yadda ake awo; ko nuna wanda ake magana a kansa; ko kuma bayanai da za su taimaka wa mai karatu a sashen Wasu Bayanai da kuma sashen Maꞌanar Kalmomi.—Matiyu 5:22, ƙarin bayani da ke kan “Gehenna.”
Sashen gaba mai jigo “Abubuwan da Za Mu Koya Daga Kalmar Allah,” yana ɗauke da muhimman koyarwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki. A ƙarshen Littafi Mai Tsarkin, akwai sashen nan “Littattafan da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki,” da kuma sashen “Maꞌanar Kalmomi da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki.” Sashen Maꞌanar Kalmomi yana taimaka wa mai karatu ya fahimci maꞌanar wasu furuci bisa ga yadda aka yi amfani da su a cikin Littafi Mai Tsarki. Sashen Wasu Bayanai yana ɗauke da: “Ƙaꞌidodin Fassara Littafi Mai Tsarki,” da “ Abubuwan da Suke Cikin Wannan Fassarar,” da “Yadda Muka Samu Littafi Mai Tsarki,” da “Sunan Allah a Cikin Nassosin Girkanci na Krista,” da “Muhimman Abubuwa da Suka Faru da Yesu Saꞌad da Yake Duniya,” da taswirori, da jadawali, da wasu bayanai da za su taimaka wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki.
Kowane littafi da ke cikin Littafi Mai Tsarki yana da sashen da ke nuna abubuwan da suke cikin surori na littafin, kuma hakan na taimaka wa mai karatu ya san taƙaitaccen abin da ke cikin littafin.

