Hausa
Muhimman Abubuwa da Suka Faru da Yesu Saꞌad da Yake Duniya—Abubuwan da Suka Faru Kafin Yesu Ya Fara Hidimarsa
https://cms-imgp.jw-cdn.org/img/p/1001061100/univ/wpub/1001061100_univ_sqr_xl.jpg
nwt pp. 484-485

A7-A

Muhimman Abubuwa da Suka Faru da Yesu Saꞌad da Yake Duniya—Abubuwan da Suka Faru Kafin Yesu Ya Fara Hidimarsa

Yadda Aka Jera Labaran da Ke Matiyu, Markus, Luka, da Yohanna

Jadawali da ke gaba suna da taswirorin da ke nuna wuraren da Yesu ya je don yin waꞌazi. Kibiyoyin da ke taswirorin ba sa nuna ainihin hanyoyin da Yesu ya bi, amma mai yiwuwa ne ya bi wurin. Harafin nan “w.” yana nufin “wajen.” Harufan nan “K.H.Y.” yana nufin “kafin haifuwar Yesu.” Harufan nan “B.H.Y.” yana nufin “bayan haifuwar Yesu.”

Abubuwan da Suka Faru Kafin Yesu Ya Fara Hidimarsa

LOKACI

WURI

ABIN DA YA FARU

MATIYU

MARKUS

LUKA

YOHANNA

3 K.H.Y.

Urushalima, haikali

Malaꞌika Jibraꞌilu ya sanar wa Zakariya haifuwar Yohanna Mai Baftisma

   

1:5-25

 

w. 2 K.H.Y.

Nazaret; Yahudiya

Malaꞌika Jibraꞌilu ya sanar wa Maryamu haifuwar Yesu; ta ziyarci danginta Alisabatu

   

1:26-56

 

2 K.H.Y.

Ƙauyen da ke tudun Yahudiya

An haifi Yohanna Mai Baftisma kuma an ba shi suna; Zakariya ya yi annabci; Yohanna zai zauna a hamada

   

1:57-80

 

2 K.H.Y., w. 1 ga Okt.

Betalami

An haifi Yesu; ‘Kalman ya zama mutum’

1:1-25

 

2:1-7

1:14

Kusa da Betalami; Betalami

Malaꞌika ya yi shelar labari mai daɗi ga makiyaya; malaꞌiku sun yabi Allah; makiyaya sun ziyarci jaririn

   

2:8-20

 

Betalami; Urushalima

An yi wa Yesu kaciya (rana ta 8); iyayensa sun kai shi haikali (bayan rana ta 40)

   

2:21-38

 

1 K.H.Y. ko 1 B.H.Y.

Urushalima; Betalami; Masar; Nazaret

Masanan taurari sun kawo ziyara; iyalin sun gudu zuwa Masar; Hirudus ya kashe yara maza; iyalin sun dawo daga Masar kuma sun zauna a Nazaret

2:1-23

 

2:39, 40

 

12 B.H.Y., Bikin Ƙetarewa

Urushalima

Yesu ɗan shekara goma sha biyu yana yi wa malamai tambayoyi a haikali

   

2:41-50

 
 

Nazaret

Ya koma Nazaret; ya ci-gaba da yi wa iyayensa biyayya; ya koyi aikin kafinta; Maryamu ta ƙara renon yara maza huɗu da mata (Mat 13:55, 56; Mrk 6:3)

   

2:51, 52

 

29, Maris-Afrilu

Daji, Kogin Jodan

Yohanna Mai Baftisma ya soma hidimarsa

3:1-12

1:1-8

3:1-18

1:6-8