Ta Hannun Yohanna 20:1-31

  • Babu kome a cikin kabarin (1-10)

  • Yesu ya bayyana ga Maryamu Magdalin (11-18)

  • Yesu ya bayyana ga almajiransa (19-23)

  • Toma ya yi shakka, amma ya ba da gaskiya daga baya (24-29)

  • Manufar wannan littafin (30, 31)

20  Da sassafe a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin ta zo kabarin, kuma ta ga cewa an riga an ture dutsen da ya rufe kabarin. 2  Sai ta gudu ta je wurin Siman Bitrus, da ɗayan almajiri wanda Yesu yake ƙauna, kuma ta ce musu: “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, kuma ba mu san inda suka ajiye shi ba.” 3  Sai Bitrus da ɗayan almajirin suka kama hanya zuwa kabarin. 4  Kuma su biyun suka soma gudu tare. Amma ɗayan almajirin ya fi Bitrus gudu, kuma ya riga shi kaiwa kabarin. 5  Da ya sunkuya ya leƙa, sai ya ga yadin lilin a cikin kabarin, amma bai shiga ciki ba. 6  Saꞌan nan Siman Bitrus ya zo a bayansa, ya shiga cikin kabarin, kuma ya ga yadin lilin a wurin. 7  Yadin da aka naɗe kansa da shi ba ya wurin da sauran yadunan suke, amma an naɗe shi an ajiye a wani gefe. 8  Sai ɗayan almajirin wanda ya fara zuwa kabarin ya shiga ciki shi ma, da ya gani, sai ya yarda. 9  Domin har ila, ba su fahimci abin da nassi ya faɗa ba cewa dole ne ya tashi daga mutuwa. 10  Sai almajiran suka koma gidajensu. 11  Amma, Maryamu ta ci-gaba da tsayawa a waje, kusa da kabarin tana kuka. Yayin da take kuka, sai ta sunkuya, ta leƙa cikin kabarin, 12  sai ta ga malaꞌiku biyu sanye da fararen riguna, suna zaune a wurin da gawar Yesu take a dā. Ɗaya yana zaune ta gefen kansa, ɗaya kuma ta ƙafafunsa. 13  Sai suka ce mata: “Me ya sa kike kuka?” Sai ta ce musu: “Sun ɗauke Ubangijina kuma ban san inda suka kwantar da shi ba.” 14  Bayan da ta faɗi wannan, sai ta juya kuma ta ga Yesu yana tsaye a wurin, amma ba ta gane cewa Yesu ne ba. 15  Sai Yesu ya ce mata: “Me ya sa kike kuka? Wane ne kike nema?” Ita kuwa tana tsammanin mai kula da lambun ne, sai ta ce masa: “Maigida, idan kai ne ka ɗauke shi, ka gaya mini inda ka kwantar da shi, domin in je in ɗauke shi.” 16  Sai Yesu ya ce mata: “Maryamu!” Da ta juya, sai ta ce masa da Ibrananci: “Rabboni!” (wanda yake nufin “Malam!”) 17  Sai Yesu ya ce mata: “Ki daina manne mini, domin ban koma wurin Uba ba tukuna. Amma, ki je wurin ꞌyanꞌuwana, kuma ki gaya musu cewa, ‘Zan koma wurin Ubana wanda Ubanku ne, da wurin Allahna wanda Allahnku ne.’” 18  Sai Maryamu Magdalin ta zo kuma ta ba almajiran labarin, ta ce musu: “Na ga Ubangiji!” Kuma ta gaya musu abin da ya gaya mata. 19  Da yamma ta yi a ranar farko ta mako, almajiran sun taru a wuri ɗaya, kuma suka rufe ƙofofi domin suna tsoron Yahudawa. Amma Yesu ya zo ya tsaya a tsakaninsu kuma ya ce musu: “Salama a gare ku.” 20  Bayan da ya faɗi wannan, sai ya nuna musu hannayensa, da kuma gefen jikinsa da aka soka. Almajiran kuma suka yi farin ciki da ganin Ubangiji. 21  Sai Yesu ya sake ce musu: “Salama a gare ku. Kamar yadda Uba ya aiko ni, ni ma ina aikan ku.” 22  Bayan da ya faɗi wannan, sai ya hura musu iska, kuma ya ce musu: “Ku karɓi ruhu mai tsarki. 23  Duk wanda kuka gafarta masa zunubai, to, an gafarta masa; kuma duk wanda ba ku gafarta masa ba, to, ba a gafarta masa ba ke nan.” 24  Amma Toma, ɗaya daga cikin almajirai goma sha biyun, wanda ake kira ꞌYan Biyu, ba ya tare da su saꞌad da Yesu ya zo. 25  Don haka, sauran almajiran suna gaya masa cewa: “Mun ga Ubangiji!” Amma ya ce musu: “In ban ga ramin* ƙusoshi a hannayensa ba, in sa yatsata a ramin ƙusoshin ba, in kuma sa hannuna a gefen jikinsa da aka soka ba, ba zan taɓa ba da gaskiya ba.” 26  Bayan kwanaki takwas, almajiran suna tare a cikin gida kuma, Toma ma yana tare da su. Sai Yesu ya shigo, duk da cewa ƙofofin suna nan a rufe, kuma ya tsaya a tsakaninsu ya ce: “Salama a gare ku.” 27  Sai ya ce wa Toma: “Ka saka yatsarka a nan, kuma ka ga hannayena, ka sa hannunka a gefen jikina da aka soka, kuma ka daina shakka, amma ka ba da gaskiya.” 28  Sai Toma ya amsa masa ya ce: “Ya Ubangijina da Allahna!”* 29  Sai Yesu ya ce masa: “Da yake ka gan ni yanzu, ka ba da gaskiya? Waɗanda ba su gan ni ba, amma duk da haka sun ba da gaskiya, suna farin ciki.” 30  Hakika, Yesu ya yi wasu abubuwan ban mamaki da yawa a gaban almajiransa waɗanda ba a rubuta a cikin littafin* nan ba. 31  Amma an rubuta abubuwan nan ne domin ku ba da gaskiya cewa Yesu shi ne Kristi, Ɗan Allah, saꞌan nan domin kuna ba da gaskiya, ku samu rai ta wurin sunansa.

Hasiya

Ko kuma “alaman.”
Wato, Mai Magana a Madadin Jehobah, da kuma Wakilinsa.
A yaren Girka, “naɗaɗɗen littafin.” Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.