Ta Hannun Yohanna 18:1-40
-
Yahuda ya ci amanar Yesu (1-9)
-
Bitrus ya yi amfani da takobi (10, 11)
-
An kai Yesu wurin Anas (12-14)
-
Lokaci na farko da Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu (15-18)
-
Yesu a gaban Anas (19-24)
-
Lokaci na biyu da na uku da Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu (25-27)
-
Yesu a gaban Bilatus (28-40)
-
“Mulkina ba na wannan duniya ba ne” (36)
-
18 Bayan da Yesu ya faɗi abubuwan nan, sai shi da almajiransa suka haye Kwarin Kidron zuwa wani wuri da akwai lambu, kuma shi da almajiransa suka shiga ciki.
2 Yahuda wanda ya ci amanar Yesu ma ya san wurin, domin Yesu ya saba haɗuwa da almajiransa a wurin.
3 Sai Yahuda ya kawo ƙungiyar sojoji, da jamiꞌan manyan firistoci da na Farisiyawa suka zo wurin riƙe da fitilu, da sandunan wuta, da kuma makamai.
4 Da yake Yesu ya san dukan abubuwan da za su faru da shi, sai ya fito gaba kuma ya ce musu: “Wane ne kuke nema?”
5 Sai suka amsa masa suka ce: “Yesu mutumin Nazaret.” Sai ya ce musu: “Ni ne shi.” Yahuda wanda ya ci amanarsa ma yana tsaye tare da su.
6 Da Yesu ya gaya musu cewa, “Ni ne shi,” sai suka ja da baya kuma suka faɗi a ƙasa.
7 Sai ya sake tambayar su kuma: “Wane ne kuke nema?” Sai suka ce: “Yesu mutumin Nazaret.”
8 Yesu ya amsa, ya ce: “Na gaya muku cewa ni ne shi. Don haka, idan ni ne kuke nema, ku bar mutanen nan su tafi.”
9 Hakan ya faru ne don a cika abin da Yesu ya faɗa cewa: “A cikin waɗanda ka ba ni, ban rasa ko guda ɗaya ba.”
10 Sai Siman Bitrus, wanda yake riƙe da takobi, ya zaro takobin, ya sari bawan shugaban firistoci, ya yanke kunnensa na dama. Sunan bawan Malkus ne.
11 Amma Yesu ya ce wa Bitrus: “Ka mai da takobin cikin gidansa. Dole ne in sha abin da ke cikin kofin da Uba ya ba ni.”*
12 Sai sojoji da shugabansu, da jamiꞌan Yahudawa suka kama Yesu kuma suka ɗaure shi.
13 Da farko sun kai shi wurin Anas, wanda shi ne baban matar Kayafas. Kayafas shi ne shugaban firistoci a shekarar.
14 Kayafas ne wanda ya shawarci Yahudawa cewa, zai fi musu amfani idan mutum ɗaya ya mutu a madadinsu.
15 Bitrus tare da wani almajirin Yesu, suna bin Yesu. Shugaban firistocin ya san ɗayan almajirin, kuma almajirin ya bi Yesu zuwa farfajiyar gidan shugaban firistocin.
16 Amma Bitrus ya tsaya a waje, kusa da ƙofar gidan. Sai ɗayan almajirin wanda shugaban firistocin ya san shi, ya fita waje kuma ya yi magana da wata baiwa da ke tsaron ƙofar, sai ya shigar da Bitrus gidan.
17 Sai baiwar ta ce wa Bitrus: “Anya, kai ba ɗaya daga cikin almajiran mutumin nan ba kuwa?” Sai Bitrus ya ce: “Aꞌa, ba na cikinsu.”
18 Da yake ana sanyi, bayin, da kuma jamiꞌan suna tsaye kewaye da wuta da suka hura da gawayi kuma suna jin ɗumi. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin ɗumin wutar.
19 Sai babban firist* ya yi wa Yesu tambaya game da almajiransa da kuma koyarwarsa.
20 Sai Yesu ya amsa masa ya ce: “Na yi magana a fili. Na yi ta koyarwa a majamiꞌa da kuma haikali, wurin da dukan Yahudawa suke taruwa, kuma babu abin da na faɗa a ɓoye.
21 Me ya sa kake yi mini tambaya? Ka yi ma waɗanda suka saurare ni tambaya a kan abin da na faɗa musu. Gama waɗannan sun san abin da na faɗa.”
22 Bayan da ya faɗi abubuwan nan, sai ɗaya daga cikin jamiꞌan da suke tsaye a wurin ya mari Yesu a fuska, kuma ya ce: “Haka ne za ka amsa wa babban firist?”
23 Sai Yesu ya amsa masa ya ce: “Idan na faɗi abin da ba daidai ba, ka gaya mini abin da ba daidai ba da na faɗa; amma idan abin da na faɗa daidai ne, to, me ya sa ka mare ni?”
24 Sai Anas ya sa aka kai Yesu a ɗaure zuwa wurin Kayafas shugaban firistoci.
25 Siman Bitrus yana tsaye a wurin, yana jin ɗumin wuta. Sai suka ce masa: “Anya, kai ba ɗaya daga cikin almajiransa ba kuwa?” Sai ya yi mūsun hakan kuma ya ce: “Ba na cikinsu.”
26 Sai ɗaya daga cikin bayin shugaban firistoci, wanda shi dangi ne ga mutumin da Bitrus ya yanke kunnensa, ya ce: “Ba na gan ka tare da shi a cikin lambun ba?”
27 Amma, Bitrus ya sake yin mūsun hakan, kuma nan da nan zakara ya yi cara.
28 Tun da sassafe, sun ɗauki Yesu daga gidan Kayafas, suka kai shi gidan gwamna, amma su da kansu ba su shiga cikin gidan gwamnan ba, domin kada su ƙazantar da kansu har su kasa cin abincin Bikin Ƙetarewa.
29 Sai Bilatus ya fito waje ya same su ya ce: “Wace ƙara ce kuka kawo a kan mutumin nan?”
30 Sai suka amsa masa suka ce: “Da a ce mutumin nan ba mai laifi ba ne, da ba mu kawo shi wurinka ba.”
31 Sai Bilatus ya ce musu: “Ku ɗauke shi, ku yi masa shariꞌa bisa ga dokarku.” Sai Yahudawan suka ce masa: “Ba mu da izinin kashe kowa.”
32 Wannan ya faru ne domin a cika abin da Yesu ya faɗa da ya nuna irin mutuwar da zai yi.
33 Sai Bilatus ya sake shiga gidan gwamnan kuma ya kira Yesu ya ce masa: “Kai ne Sarkin Yahudawa?”
34 Sai Yesu ya amsa ya ce: “Kana tambayar nan don kana so ka sani ne, ko kuma wasu ne suka gaya maka game da ni?”
35 Sai Bilatus ya amsa ya ce: “Ni ba Bayahude ba ne. Mutanenka da kuma manyan firistoci ne suka kawo ka wurina. Mene ne ka yi?”
36 Yesu ya amsa ya ce: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne, da a ce Mulkina na duniyar nan ne, da masu yi mini hidima sun yi faɗa don kada a miƙa ni ga Yahudawa. Amma yanzu Mulkina ba daga nan yake ba.”
37 Sai Bilatus ya ce masa: “To, kai sarki ne?” Sai Yesu ya amsa ya ce: “Kai da kanka ka ce ni sarki ne. Wannan ne ya sa aka haife ni, kuma shi ya sa na zo cikin duniya, domin in ba da shaida ga gaskiya. Kuma duk wanda yake na gaskiya yakan saurari muryata.”
38 Sai Bilatus ya ce masa: “Mece ce gaskiya?”
Bayan da ya faɗi hakan, sai ya sake fita waje wurin Yahudawan kuma ya ce musu: “Ban same shi da wani laifi ba.
39 Ƙari ga haka, kuna da wata alꞌada cewa in sako muku wani mutum a lokacin Bikin Ƙetarewa. Don haka, kuna so in sake muku Sarkin Yahudawa ne?”
40 Sai suka sake ta da murya, suna cewa: “Aꞌa, ba mutumin nan za ka sako mana ba, sai dai ka saki Barabbas!” Barabbas kuwa wani ɗan fashi ne.
Hasiya
^ A yaren Girka, “Ba dole ne in sha abin da ke cikin kofin da Uba ya ba ni ba?”
^ Wato, Anas.